31 Agusta 2020 - 13:29
Rikicin kabilanci ya yi Ajalin mutum 3 A Sudan

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu wasu 11 na daban suka samu raunuka a wani rikicin kabilanci da ya kunno kai a kasar Sudan a ranar Alhamis da ta gabata.

ABNA24 : Taho mu gamar ya faru ne tsakanin ‘yan kabilar Beni Amer da na Beji sakamakon zabar Salah Ammar daga kabilar Beni Amer a matsayin sabon gwamnan jihar Kassala da ke gabashin kasar.

Dubban mutane sun fito da sanduna da wukake da takubba a jihar ta Kassala domin nuna rashin amincewarsu da zaben da aka ce an yi wa Salah Ammar, inda suke zargin an tafka magudi a zaben.

Jami’an tsaron Sudan sun yi nasarar kama wasu mutane bakwai a matsayin wadanda suka ruruta wutan rikicin. Kamar yadda gwamnatin kasar ta aike da tawagar jami’an tsaro zuwa jihar da Kassala domin shawo kan rikicin tare da kafa dokar ta baci.

Tun a watan Yulin wannan shekara ce fira ministan Sudan Abdallah Hamdok ya sanar da aniyarsa na sauya gwamnoni a Sudan daga sojoji zuwa fararen hula a dukkanin jihohin kasar 18 amma matsalar kabilanci take neman kawo cikas ga wannan shiri na gwamnatin Hamdok.

342/